Wasanni

Barcelona ta soma laluben wanda zai maye gurbin kocinta

Kocin kungiyar Barcelona Ernesto Valverde.
Kocin kungiyar Barcelona Ernesto Valverde. REUTERS/Phil Noble

Rahotanni daga kafafen yada labaran kasar Spain sun ce kungiyar Barcelona ta soma kokarin tantance sabon mai horaswar da zai maye gurbin kocinta na yanzu, Ernesto Valverde.

Talla

Matakin na Barcelona ya biyo bayan rashin tabbas din ci gaba da aikin Valverde, mai horar da yan wasan nata na yanzu, wanda ya taimaka mata lashe kofin gasar La Liga na bana.

Sai dai duk da nasarar lashe gasar ta La Liga, Barcelona ta gaza lashe kofin gasar Copa del Rey, a karshen makon da ya gabata, zalika kungiyar ta gaza kaiwa wasan karshe na gasar zakarun Turai, bayan da Liverpool ta lallasa ta da 4-0, duk da cewa a zagayen farko, Barcelona ke jagoranci da 3-0.

Yanzu haka dai rahotanni sun ce kungiyar ta Barcelona ta zayyana wadanda take sa ran za su maye gurbin kocinta Ernesto Valverde.

Kwararrun masu horaswar da Barcelona ke zawarci sun hada da, Kocin Arsenal Unai Emery,kocin tawagar kwallon kafa ta kasar Holland Ronald Koeman, mai horas da Juventus Massimiliano Allegri da kuma tsohon kocin Everton Roberto Martinez.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.