Wasanni

Chelsea ta saidawa Real Madrid Hazard kan euro miliyan 115

Eden Hazard.
Eden Hazard. REUTERS/Hannah Mckay

Kungiyar Chelsea ta tabbatar da cimma yarjejeniyar saidawa Real Madrid dan wasanta Eden Hazard kan cinikin euro miliyan 115.

Talla

Sai dai Real Madrid za ta soma mikawa Chelsea euro miliyan 100, idan kwalliya ta soma biyan kudin sabulu kuma kan sayen Hazard din to Madrid za ta cika euro miliyan 15.

Tun a shekarar 2018, Hazard ya so komawa Real Madrid, amma kocin Chelsea Maurizio Sarri, ya roke shi da ya dakata har zuwa bayan shekara guda, kafin rabuwa da kungiyar.

Karkashin yarjejeniyar da aka cimma, Real Madrid za ta rika biyan Hazard fam dubu 400,000 a mako daya, albashin da ya zarta wanda dan wasan ke karba a Chelsea na fam dubu 300,000 a mako guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI