Wasanni

Gasar zakarun Turai: Liverpool ta karbi kyautar euro miliyan 108

Yan wasan Liverpool yayin murnar lashe kofin gasar Zakarun Turai na 2019.
Yan wasan Liverpool yayin murnar lashe kofin gasar Zakarun Turai na 2019. REUTERS/Carl Recine

Liverpool ta samu kyautar euro miliyan 108, kwatankwacin naira biliyan 43 da miliyan 438 da dubu 680, bayan samun nasarar lashe kofin gasar zakarun kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar Turai.

Talla

Yayin wasan na ranar Asabar da aka fafata a birnin Madrid da ke Spain, Liverpool ta doke Tottenham da kwallaye 2-0, ta hannun ‘yan wasanta Muhd Salah da Divock Origi.

A shekarar bara, Liverpool ta samu nasarar kaiwa zagayen karshe na gasar ta Zakarun Turai, amma Real Madrid mai rike da kofin gasar a waccan lokacin, ta doke ta da kwallaye 3-1.

Karo na shida kenan da Liverpool ke samun nasarar lashe kofin gasar zakarun Turai, wanda a halin yanzu, kungiyoyin Real Madrid, da AC Milan ne kawai ke gaban Liverpool din wajen yawan kofunan na zakarun Turan da suka lashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI