Wasanni

Messi ya bukaci Barcelona ta yi watsi da shirin sayen Griezmann

Kaftin din Barcelona Lionel Messi, yayin gaisawa dan wasan Atletico Madrid Antoine Griezmann.
Kaftin din Barcelona Lionel Messi, yayin gaisawa dan wasan Atletico Madrid Antoine Griezmann. REUTERS

Kaftin din Barcelona Lionel Messi, ya bukaci kungiyar ta yi watsi da batun sayen dan wasan Atleico Madrid Antoine Griezmann.

Talla

A baya bayan nan dai, an sha alakanta Griezmann da komawa Barcelona, bayan da ya bayyana aniyar rabuwa da kungiyarsa a bana.

A 2018 Barcelona ta yi kokarin sayen Griezmann amma yayi watsi da tayinta.

Messi ya ce a maimakon sayen Griezmann, kamata yayi Barcelonan ta maido da Neymar, dan wasanta da ta saidawa PSG kan cinikin euro Fammiliyan 198 a shekarar 2017.

Tun bayan saida Neymar ga PSG, Barcelona ke fafutukar maye gurbinsa, kuma a kokarin hakan ne, kungiyar ta sayi Philippe Coutinho daga Liverpool da kuma Ousmane Dembele daga Borrussia Dortmund, amma har yanzu yan wasan biyu, sun gaza nuna kwazon da ake bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI