Real Madrid ta cefano zaratan 'yan wasa 4
Wallafawa ranar:
Real Madrid na ci gaba da shirin farfadowa daga suman da ta yi a duniyar kwallo, bayan da a ranar laraba ta kammala cinikin sayen Ferland Mendy daga kungiyar Lyon, mai tsaron baya daga bangaren hagu.
A karkashin yarjejeniyar da suka kulla, Mendy wanda ya koma Real Madrid kan euro miliyan 50 zai bugawa kungiyar wasanni tsawon shekaru 6.
A ranar 19 ga watan Yuni kuma za a gabatar da Mendy mai shekaru 24 ga magoya baya, hakan na nufin dan wasan zai yi gogayya da Marcelo a bangaren tsaron bayan Real Madrid.
Zuwa yanzu dai kungiyar ta sayi zaratan ‘yan wasa 4 kenan a kokarin da Zinaden Zidane ke yi na maido da karsashin da ta rasa.
Bayan kashe jimillar euro miliyan 300, a halin yanzu Real Madrid ta sayi ’yan wasan da suka hada da Luka Jovic adag Frankfurt, Eden Hazard daga Chelsea, Eder Militao daga FC Porto sai kuma Ferland Mendy daga Lyon.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu