Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne game da gasar kwallon kafa ta jami'o'in Najeriya da za a fara gudanarwa a ranar 18 ga watan Yunin 2019, inda jami'o'i 32 za su fafata da juna, yayinda za a shafe tsawon makwanni 21 kafin kammala gasar baki daya. Kuna iya latsa hoton labarin domin sauraren cikakken shirin.