Mutuwar Morsi ba za ta shafi gasar cin kofin Afrika ba -Masar
Wallafawa ranar:
Masu shirya gasar cin kofin Afrika can a Masar sun bayyana cewa mutuwar tsohon shugaban kasar ba zai shafi tsare-tsaren gasar ba, haka zalika ba zai sanya sauya lokaci ko kuma dage fara gasar wadda za a fara gudanar da ita cikin makon nan ba.
Akwai dai jita-jitar da ke bayyana cewa Masar za ta dage ko kuma sauya lokacin wasanta da Zimbabwe a ranar juma’a mai zuwa wanda da shi ne za a bude wasannin gasar, sai dai wani babban jami’in hukumar kwallon kafar kasar ya ce jimamin mutuwar ba zai shafi wasannin gasar ba.
A ranar juma’a 21 ga wata ne dai za a bude gasar ta cin kofin Afrika, gasar da kasashen nahiyar 24 za su halarta cikin rukuni 6 da ya kunshi kasahen hur-hudu, ciki kuwa har da kamaru mai rike da kambun wadda ke rukunin F wanda ya kunshi kasashen Benin, Ghana da kuma Guinea Bissau.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu