Wasanni

Najeriya ta shiga tsaka mai wuya bayan shan kaye a hannun Faransa

'Yar wasan Faransa Wendy Renard yayin bugun daga kai sai mai tsaron raga da ta jefa kwallo a ragar Super Falcons ta Najeriya.
'Yar wasan Faransa Wendy Renard yayin bugun daga kai sai mai tsaron raga da ta jefa kwallo a ragar Super Falcons ta Najeriya. AFP / Franck Fife

Najeriya ta yi rashin nasara a wasan karshe na matakin rukunin farko da take ciki, inda mai masaukin baki Faransa ta samu nasara kanta da 1-0, a gasar cin kofin duniya ta mata da ke gudana.

Talla

Najeriya dai na bukatar yin koda maki daya ne a wasan, ta hanyar tashi kunnen doki ko canjaras tsakaninta da mai masaukin baki Faransa, domin tsallakawa zuwa zagaye na gaba a gasar.

A mintuna na 75 Faransa ta samu damar bugun daga kai sai mai tsaron raga, ta zubar, amma alkalin wasa Melissa Paola Borjas ta bada umarnin a sake bugun faneretin, wanda kuma yar wasan Faransa Wendie Renard ta samu nasarar jefa kwallon a damar ta biyu.

A halin yanzu Najeriya za ta jira zuwa ranar 20 ga watan Yuni, alhamis mai zuwa kenan, lokacin da za’a kammala buga wasannin matakin rukuni domin sanin ko za ta samu damar tsallakawa zuwa zagaye na 2 na gasar ta cin kofin duniya, idan har  tana kan gaba tsakanin kasashen da suka kammala wasannin rukuni a matsayi na 3 da yawan kwallaye, da kuma karancin wadanda aka jefa mata a raga.

Kasashen hudu da suka kammala wasannin rukuninsu da maki mai yawa ake bukata zuwa zagaye na gaba, kuma China ta kame guda daga ciki.

A yanzu Najeriya na bukatar Scotland ta lallasa Argentina,ko kuma su tashi canjaras, zalika tana bukatar New Zealand ta tashi kunnen doki da kamaru, ko kuma duk wanda ya samu nasara,to kada ya ci kwallaye sama da 3, sai kuma bukatar da Super Falcons na Najeriya keda ita, wajen ganin Jamaica ta lallasa Australia a rukuni na uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.