"Barcelona ce ta fi dacewa da Salah na Liverpool"
Wallafawa ranar:
Tsohon dan wasan Chelsea, Samuel Eto’o ya bukaci Mohamed Salah na Masar da ya sauya sheka daga Liverpool ta Ingila zuwa Barcelona a Spain.
Tun shekarar 2017 Salah ke taka rawar gani a Liverpool, inda ya ci mata kwallaye 54 a cikin wasanni 74.
An dai yi ta rade-radin cewa, Salah zai koma Real Madrid amma, Eto’o na ganin cewa, Barcelona ce za ta fi dacewa da dan wasan na Liverpool.
Eto'o wanda ya yi shekaru biyar a Barcelona tun daga shekarar 2004, ya ce, Real Madrid ce silar tafiyarsa Turai daga Afrika, amma yana da masaniya kan tsarin Barcelona, don haka kungiyar ce tafi dacewa da Salah
Eto'o ya ce, Salah na da duk abinda ake bukata domin zama daya daga cikin zaratan ‘yan wasan kwallon kafa na duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu