Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi nazari ne kan kasashen da za su iya lashe gasar cin kofin Afrika da ke gudana a Masar. Masana kwallon kafa a Afrika irinsu Kanu Nwanko da Daniel Amokachi da Garba Lawan sun shaida wa RFI Hausa hasahensu game da gasar. Kuna iya latsa kan hoton domin sauraren cikakken shirin.