Wasanni-Kwallon kafa

Kamaru ka iya fuskantar chukuncin FIFA kan rashin da a

Tambarin gasar cin kofin duniya na mata da ke gudana Faransa
Tambarin gasar cin kofin duniya na mata da ke gudana Faransa RFI

Da alamu kungiyar kwallon kafar Kamaru bangaren mata ka iya fuskantar ladabtar daga abin da wasu mahukuntan kwallon kafa ke kira da rashin da’ar da ta nuna yayin gasar cin kofin duniya bangaren mata bayan rashin nasararta hannun Ingila da kwallaye 3 da nema a zagayen kasashe 16.

Talla

Yayin wasan na ranar Lahadi dai sau biyu tawagar ‘yan wasan ta Kamaru na tilasta dakatar da wasan na dan wani lokaci kafin ci gaba, inda a bangare guda fada ya barke tsakanin ‘yar wasan gaba ta Kamaru Augustine Ejangue da takwararta ta Ingila Toni Duggan.

Batun dai na daga cikin batutuwan da hukumar FIFA za ta yi zama na musamman a kansu bayan karkare gasar, ko da dai kawo yanzu hukumar ta FIFA ba ta bayyana ko za ta dauki matakin ladabtarwa kan tawagar ta Kamaru ba.

Sai dai a bangare guda shugabar kwamitin da ke kula da kwallon mata karkashin hukumar kwallon kafar Afrika Isha Johansen ta ce ta na duba yiwuwar daukar matakan ladabtarwa kan Kamarun, la’akari da cewa rashin da’ar da ta nuna ya bata sunan hatta sauran tawagar kwallon kafar Afrika ba kadai kuma bangaren mata ba.

Yayin wasan dai an ga yadda aka samu musayar yawu hatta tsakanin mai horar da kungiyar kwallon kafar ta Kamaru da alkalin wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.