Wasanni

Za mu gyara kuskurenmu a wasanmu na gaba- Mikel Obi

Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Mikel Obi
Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Mikel Obi REUTERS/Matthew Childs

Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Mikel Obi ya ce caccakar da tawagar ta ke sha daga magoya bayanta bayan shan kayenta a hannun Madagascar da kwallaye 2 da nema, na da nasaba da fatan da kasar ke da shi wajen ganin sun kai ga nasarar dage kofin a wannan karon.

Talla

A cewarsa, caccakar na zuwa daga masoyan Super Eagles masu yi mata fatan alkhairi da kuma neman ci gaban ta, don haka za ta kara musu karsashin ganin sun fitar da Najeriyar kunya a wasannin gaba.

Rashin nasarar ta Najeriya hannun Madagascar dai ya sanya ta kammala wasanta na rukuni a matsayin ta 2, wanda hakan ke nuna cewa za ta hadu da Ghana a wasanta na zagayen kungiyoyi 16 a karon farko, wanda kuma ke matayin babban kalubale ga kasar matukar ba ta sauya salon wasanta ba.

Kaftin din na Super Eagles Mikel Obo ya ce, sun amsa laifin ba su yi abin kirki a wasan ba, amma ya na fatan a karawarsu ta gaba sun sanya ‘yan Najeriya Farin ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI