Wasanni

Sai mun ga abinda ya turewa buzu nadi akan Pogba - Real Madrid

Paul Pogba.
Paul Pogba. Reuters

Rahotanni daga Ingila sun ce kowane lokaci daga yanzu, dan wasan Manchester United Paul Pogba, zai mikawa kungiyar bukatar neman rabuwa da ita a hukumance.

Talla

Jaridar Mundo Deportivo da ke Spain ta rawaito kungiyar Real Madrid na cewa ko da Pogba bai mika bukatar rabuwa da United ba, za ta ci gaba da matsawa kan sayen dan wasan, har sai hakarta ta cimma ruwa.

A baya bayan nan Real Madrid ta gabatarwa da United tayin biyanta euro miliyan 80 da kuma mika mata zabin yan wasanta Gareth Bale ko kuma Isco, a matsayin musayar Pogba, amma Manchester United ta noke.

Itama dai tsohuwar kungiyar Pogba, wato zakarar gasar Seria A, Juventus, ta nemi maido da dan wasan, inda ta gabatar da tayin biyan miliyan 70, da kuma mikawa United dan wasanta Poulo Dybala, Alex Sandro ko kuma Blaise Matuidi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.