Wasanni

Dangantaka na dada yin tsami tsakanin Neymar da PSG

Dan wasan kungiyar PSG, Neymar.
Dan wasan kungiyar PSG, Neymar. REUTERS/Charles Platiau

Baraka na ci gaba da bayyana tsakanin tauraron kwallon kafar Brazil Neymar da Silva da kungiyarsa ta PSG.

Talla

Tsamin dangantakar ta dada bayyana ne, bayanda dan wasan ya yi kakkausan suka ga shugabancin kungiyar ta PSG, bisa sanarwar da ta fitar cewa, yaki halartar atasayen wasannin sharer fage na soma kakar wasa ta bana, zargin da yayi watsi da shi.

Yayinda shi ma yake tsokaci kan takaddamar, mahaifin Neymar ya kare dan nasa da cewa, PSG ta dade da sanin sai a ranar 15 ga watan Yuli dan wasan zai koma fagen atasaye, amma ta sanar cewa, yaki zuwa da gangan har ma take ikirarin daukar matakin ladabtarwa.

Takun saka tsakanin Neymar da PSG na ci gaba daidai lokacin da batun komawa tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona ke dada karfi, duk da cewa komen ya raba kan wasu daga cikin shugabannin tsohuwar kungiyar tasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI