Wasanni-Kwallon kafa

Origi na Liverpool ya tsawaita kwantiraginsa a Club din

Divock Origi yayin wasan gab da na karshe da Liverpool ta lallasa Barcelona da kwallaye 4 da nema
Divock Origi yayin wasan gab da na karshe da Liverpool ta lallasa Barcelona da kwallaye 4 da nema REUTERS/Phil Noble

Dan wasan Liverpool Divock Origi ya sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita kwantiraginsa da Club din.

Talla

Origi dan asalin kasar Kenya da ke taka leda a kungiyar kwallon kafar kasar Belgium tun a shekarar 2014 ya kulla kwantiragin shekaru 5 da Liverpool kan yuro miliyan 10 amma ya shafe tsawon kakar wasa 2 a matsayin aro can a Lille ta Faransa.

Sai dai dawowarsa tawagar ta Liverpool cikin watan Disamban bara ya bayar da gagarumar gudunmawa ga nasarar Liverpool a gasar cin kofin zakarun Turai, musamman wasansu da Barcelona inda ya zura kwllaye 2 da kuma wasan karshe da shima ya yi nasarar zura kwallo guda da ya basu damar dage kofin gasar.

Cikin kakar wasa biyu dai Origi ya zura kwallaye 21 a bangaren Liverpool.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.