Wasanni-Kwallon kafa

Senegal ta lallasa Benin da kwallo 1 mai ban haushi

Cebio Soukou yayin wasa tsakanin Benin da Senegal
Cebio Soukou yayin wasa tsakanin Benin da Senegal RFI/Pierre René-Worms

Senegal ta lallasa Benin da kwallo 1 mai ban haushi, duk dai a wasannin gasar cin kofin Afrikan da ya gudana jiya.

Talla

Yayin wasan tsakanin Benin da Senegal an yi ta fafatawa har zuwa dawowa daga hutun rabin lokaci ba tare da wani bangare ya yi nasara ba, kafin daga bisani, Idrissa Gana Gueye ya zurawa Senegal kwallonta daya tal a minti na 70 da fara wasa.

Su ma dai yayin wasan na su a bangren Benin ‘yan wasan irinsu Cebio Soukou da Steve Mounie sun samu katin gargadi, yayinda Oliver Verdon kuma ya samu jan kati dungurugum, a bangaren Senegal kuma dan wasan gaba na Liverpool Sadio Mane ya samu na shi katin gargadin.

Yanzu haka dai Senegal za ta kara ne da ko dai Madagascar ko kuma Tunisia a wasanta na gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.