Wasanni-Kwallon kafa

Super Eagles ta fitar da Bafana Bafana daga gasar cin kofin Afrika

Dab wasan Najeriya William Troost-Ekong bayanzura kwallo a minti na 89 da ya bai wa Super Eagles damar fitar da Afrika ta kudu daga gasar ta cin kofin Afrika.
Dab wasan Najeriya William Troost-Ekong bayanzura kwallo a minti na 89 da ya bai wa Super Eagles damar fitar da Afrika ta kudu daga gasar ta cin kofin Afrika. REUTERS/Amr Abdallah Dalsh

Super Eagles ta Najeriya ta lallasa Bafana ta Africa ta kudu da kwallo 2 da 1 a wasan gab da na kusa da na karshe na cin kofin Afrika da ke ci gaba da gudana can a kasar Masar.

Talla

Yayin wasan na daren jiya wanda ya gudana a filin wasa na birnin Cairo, Super Eagles ce ta fara zura kwallon farko a raga ta hanyar dan wasanta Samuel Chukwuze a minti na 27 da fara wasa, ba tare da Bafana ta farke ba har zuwa tafiya hutun rabin lokaci.

A minti na 71 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne, Bafana ta farke kwallon ta hannun dan wasanta Bongani Zungu amma Dan wasan Najeriya William Troost-Ekong ya kara kwallo ta biyu a minti na 89 gab da karkare wasa, matakin da ya bai wa Super Eagles din gagarumar nasara kan Bafana.

Bafana ta Afrika ta kudu wadda ta fitar da mai masaukin baki Masar daga gasar, dama a tarihin kwallo tun daga 1992 sau biyu cal ta taba yin nasara akan Najeriya cikin haduwa 14 da suka yi a manyan wasanni.

Yayin wasan dai akalla ‘yan wasan Bafana 4 ne suka samu katin gargadi ciki har da Percy Tau, yayinda Ahmad Musa a bangaren Najeriya shi ma ya samu nasa katin gargadin wato Yellow Card.

A wasan gaba da zai gudana ranar Lahadi dai Najeriyar za ta fuskanci ko dai Ivory Coast ko kuma Algeria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.