Wasanni

Sayen Griezmann ya tilasta mana karbar bashi - Barcelona

Kungiyar Barcelona ta sanar da cewa, sai da ta karbi bashin kudade kafin samun damar sayen Antione Griezmann daga Atletico Madrid kan euro miliyan 120.

Sabon dan wasan Barcelona Antoine Griezmann da Neymar, tsohon dan wasan kungiyar.
Sabon dan wasan Barcelona Antoine Griezmann da Neymar, tsohon dan wasan kungiyar. YouTube
Talla

A ranar lahadi da ta gabata Barcelona ta yi bikin nuna Griezmann ga magoya bayanta.

Sanarwar ta Barcelona na nuna a halin yanzu ba ta da kudin sayen karin 'yan wasa a nan kusa, abinda ya jefa yunkurin da Neymar ke yi na yi mata kome daga PSG cikin Shakku.

A 2017 bakwai Barcelona tasaidawa PSG Neymar kan euro miliyan 222, sai dai tun kafin sauyin shekar ya cika shekaru biyu, dan wasan da yayi ta fama da samun rauni, ya soma nadamar rabuwa da tsohuwar kungiyar tasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI