Wasanni

Daniele de Rossi ya koma kungiyar Boca Juniors

Tsohon dan wasan kungiyar AS Roma Daniele De Rossi.
Tsohon dan wasan kungiyar AS Roma Daniele De Rossi. REUTERS/Miguel Vidal

Tsohon dan wasan AS Roma kuma daya daga cikin taurarin Kungiyar da ya raba gari da ita a karshen kakar wasa da ta gabata, Daniele de Rossi, ya koma kungiyar Boca Juniors da ke Argentina.

Talla

Za a iya cewa de Rossi mai shekaru 36 ya kammala dukkanin kwalllonsa ce a AS Roma, wadda ya bugawa jimillar wasanni 616 ya kuma ci mata kwallaye 63.

Dan wasan shi ne na biyu da ya bugawa AS Roma adadin wasanni mafi yawa, bayan tsohon dan wasanta Fransisco Totti da ya buga mata wasanni 768.

Kafin sauya sheka zuwa Boca Juniors, kungiyar ta AS Roma ta yiwa de Rossi tayin bashi mukamin daraktan wasanninta, amma ya noke, inda yace har yanzu yana jin kansa a matsayin dan wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.