Wasanni

Darasin da kasashen Afrika suka dauka bayan gasar AFCON

Sauti 10:10
Kasashen Afrika 24 suka fafata da juna a gasar cin kofin Afrika da aka gudanar a  Masar
Kasashen Afrika 24 suka fafata da juna a gasar cin kofin Afrika da aka gudanar a Masar Bien Sports

Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya waiwayi Gasar Cin Kofin Afrika ne da aka kammala a Masar, inda ya duba darasin da kasashen Afrika ya dace su dauka bayan kammala gasar. Kazalika shirin ya tabo wani bangare na jadawalin kasashen da suka fi iya taka leda a duniya da FIFA ta fitar a baya-bayan nan.