Wasanni

Real Madrid ta dakatar shirin sayar da Bale

Gareth Bale.
Gareth Bale. REUTERS/Wolfgang Rattay

Real Madrid ta soke shirin saida dan wasanta Gareth Bale ga kungiyar Jiangsu Suning da ke China, yarjejeniyar da a baya ke gaf da tabbata.

Talla

A baya an sa ran Bale, mai shekaru 30 zai sauya sheka zuwa gasar kwallon kafa ta China kan yarjejeniyar shekaru 3, inda za a rika biyansa fam miliyan a duk mako, kwatankwacin naira miliyan 444 da dubu 985.

Soke shirin saida Bale na nuni da cewa dan wasan ka iya samun damar karasa yarjejeniyar shekaru 3 data rage tsakaninsa da Real Madrid, duk da cewa alamu sun nuna kocin kungiyar Zinaden Zidane baya bukatar kasancewarsa cikin sabuwar tawagar da yake ginawa.

A shekarar 2013 Bale ya koma Real Madrid daga Tottenham kan fam miiyan 85, mafi tsada a waccan lokacin, kuma tare da shi kungiyarta yi nasarar lashe jimillar kofuna 12, da suka hada kofin gasarzakarun Turai 4, La liga 1, Copa del Rey 1, kofunan gasar UEFA Super Cup 3 da kuma na Club World Cup 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.