Wasanni

Mai yiwuwa Adebayor ya sake haskawa a gasar Premier

Emmanuel Adebayor.
Emmanuel Adebayor. Reuters

Rahotani sun ce dan wasan gaba na kasar Togo Emmanuel Adebayor na shirin komawa gasar Premier ta Ingila nan bada jimawa ba.

Talla

A yanzu haka dai babu wata yarjejeniya tsakanin Adebayor da wata kungiya, bayan karewar wa’adin zamansa da kungiyar Basaksehir da ke Turkiya.

Majiyoyi masu tushe sun rawaito cewar, kungiyoyin da suka hada da Watford, West Ham da Sheffield United ne ke zawarcin tsohon tauraron kungiyar Arsenal, wanda kuma ya bugawa Tottenham, Manchester City da kuma Crystal Palace.

Adebayor ya ci jimillar kwallaye 97 a tsawon lokacin da ya shafe yana haskawa a Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI