Isa ga babban shafi
Wasanni

A shirye muke mu biya euro miliyan 166 kan Pogba - Madrid

Dan wasan Manchester United Paul Pogba.
Dan wasan Manchester United Paul Pogba. Reuters
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Kungiyar Real Madrid ta ce a shirye take ta mikawa Manchester United euro miliyan 166 kan dan wasanta Paul Pogba, kamar yadda jaridar 'The Sun' dake Ingila ta rawaito.

Talla

Madrid na kokarin ganin wannan ciniki ya tabbata ne kuma kafin rufe hada hadar sauin shekar ‘yan wasa a wata mai kamawa.

A baya kungiyar ta Real Madrid ta yi yunkurin gamsar da United kan saida mata Pogba ta hanyar mika mata kudi hadi da wasu ‘yan wasanta uku, da suka hada da Gareth Bale, James Rodriguez da kuma mai tsaron raga Keylo Navas.

Tun bayan sake karbar aikin horas da Real Madrid da Zidane yayi, kocin ke fafutukar ganin ya farfado da kungiyar daga dogon suman da ta yi musamman a kakar wasan da ta gabata, inda ta gaza lashe kofin La liga, Copa del Rey da kuma kare kabinta na zakarar gasar kungiyoyin nahiyar Turai.

Zuwa yanzu dai Real Madrid ta sayi manyan yan wasan da suka hada da Hazard daga Chelsea, Luka Jovic daga Frankfurt, Eder Militao daga Porto, Rodrygo daga Santos, da Ferland Mendy daga Lyon, amma hakan bai hana abokiyar hamayyarta Atletico Madrid lallasa ta da 7-3, a makon jiya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.