Wasanni

Neymar ya kauracewa wasannin PSG

Dan wasan kungiyar PSG Neymar.
Dan wasan kungiyar PSG Neymar. REUTERS/Nacho Doce

Rahotanni sun ce dagantaka ta kara yin tsami tsakanin Neymar da kungiyarsa PSG, bayan da dan wasan ya ce ba zai kara buga mata wasa ba.

Talla

Matakin na Neymar sabon yunkuri ne na tilastawa PSG kyale shi ya koma tsohuwar kungiyarsa Barcelona, wadda a baya bayan nan tayi kokarin sake dawo da shi, ta hanyar tayin mikawa PSG kudi da wasu ‘yan wasanta, amma kungiyar ta noke, inda ta kafe kan cewa sai an biya ta kudin da yayi kusa da euro miliyan 222 da ta biya kan Neymar a 2017.

A halin yanzu majiyoyi da dama sun rawaito cewar, Neymar na yin atasaye shi kadai ba tare da tawagar kungiyar tasa ta PSG ba.

Zalika tun bayan dawowa daga hutu, Neymar bai bugawa kungiyar wasa ba, kuma ga dukkanin alamu dan wasan yayi tsayuwar gwamen jaki kan aniyarsa ta tilastawa PSG kyale shi yiwa tsohuwar kungiyarsa kome.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI