Wasanni

Pepe ya kafa tarihin zama dan wasan Arsenal mafi tsada

Nicolas Pepe, tsohon dan wasan gaba na kungiyar Lille da ya kafa tarihin zama dan wasa mafi tsada da Arsenal ta taba saya.
Nicolas Pepe, tsohon dan wasan gaba na kungiyar Lille da ya kafa tarihin zama dan wasa mafi tsada da Arsenal ta taba saya. REUTERS/Pascal Rossignol

Nicolas Pepe ya kafa tarihin zama dan wasa mafi tsada da Arsenal ta saya a tarihinta bayan Pierre Emerick Aubamayang daga Borussia Dortmund kan fam miliyan 56 a watan Janairun 2018.

Talla

A ranar Alhamis Arsenal ta bayyana sayen Pepe dan wasan gaba na Lille kuma tauraron kungiyar kan fam miliyan 72; dala miliyan 87 kenan.

Sabon dan wasan na Arsenal na daga cikin wadanda manyan kungiyoyi a nahiyar Turai ke fafutukar kulla yarjejeniya da shi, la’akari da bajintarsa a kakar wasa ta bara, inda ya ci wa kungiyarsa ta Lille da ke gasar League 1 ta Faransa kwallaye 23, ya kuma taimaka wajen jefa wasu 12, cikin wasanni 41 da ya buga.

Daga cikin kungiyoyin da suka yi kokarin sayen Nicolas Pepe akwai Manchester United da kuma Napoli.

Kamar yadda muka bayyana a baya, tsohon dan wasan Borussia Dortmund Pierre-Emerick Aubameyang, shi ne dan wasa na biyu mafi tsada da Arsenal ta saya kan fam miliyan 56, biye da shi kuma Alexander Lacazette ne da Arsenal ta sayo daga Lyon kan fam miliyan 47, kuma a kakar wasa ta bara magoya bayan Arsenal sun zabe shi a matsayin dan wasan kungiyar mafi kwazo.

Mesut Ozil da Arsenal ta saya kan fam miliyan 43 daga Real Madrid a 2013, shi ne dan wasan kungiyar na 4 mafi tsada, kuma na farko mafi tsadar da ta saya a karkashin tsohon kocinta Arsene Wenger.

Dan wasa na biyar kuwa shi ne Shkodran Mustafi daga Valencia da Arsenal ta kulla yarjejeniya da shi kan fam miliyan 35.

Granit Xhaka, Alexis Sanchez da William Saliba da Arsenal ta saya kan fam miliyan 34, 32 da kuma 27 sune ‘yan wasa na 6,7 da kuma 8 mafiya tsada da kungiyar ta kulla yarjejeniya da su, yayinda Lucas Torriera da ta saya kan fam miliyan 26 daga Sampdoria da mai tsaron raga Bernd Leno daga Bayer Leverkusen kan fam miliyan 22, ke matsayi na 9 da kuma 10.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI