Wasanni

Messi zai yi jinyar makwanni 2

Kaftin din Barcelona Lionel Messi.
Kaftin din Barcelona Lionel Messi. Phil Noble/Reuters

Mai yiwuwa kaftin din Barcelona Lionel Messi ba zai samu hasakawa a wasan farko da kungiyar za ta soma a kakar wasa ta bana ba, sakamakon raunin da ya samu a kafa.

Talla

Bayan gudanar da bincike kan raunin, likitoci sun ce Messi zai shafe akalla makwanni 2 kafin murmurewa.

A halin yanzu kasa da makwanni 2 ya rage Barcelona ta fatata wasan farko na gasar La liga a kakar wasa ta bana tsakaninta da Athletic Bilbao ranar 16 ga watan Agustan da muke ciki, 2019.

Tuni kuma kungiyar Barcelona ta sanar da cewa Messi baya cikin tawagarta da za su fafata wasan sada zumunci da kungiyar Napoli a Florida, a ranar laraba mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.