Wasanni-Kwallon kafa

Manchester United za ta hukunta Romelu Lukaku

Dan wasan Manchester United Romelu Lukaku
Dan wasan Manchester United Romelu Lukaku REUTERS/Marcos Brindicci

Kungiyar kwallon kafa, ta Manchester United ta ce za ta ci tarar dan wasanta Romelu Lukaku saboda kauracewa halartar atisayen da ya yi, ba kuma tare da bayyana dalili ba.

Talla

Lukaku dan Belgium mai shekaru 26 kwana biyu kenan yana kin halartar atisayen Man United inda ya ke nasa atisayen daban can a tsohon club dinsa Anderlecht.

Kungiyoyin Italiya 2 ne dai ke zawarcin Lukaku da suka kunshi Inter Milan da Juventus, sai dai dan wasan ya fi son ya je Inter Milan yayinda shi kuma Club din na sa yafi kaunar ya je Juventus.

Lukaku wanda ya gaza halartar ko da daya daga cikin wasannin tunkarar sabuwar kakar ad Manchester United ta doka saboda raunin da yak e fama da shi, yanzu haka dillalinsa Federico Pastorello na tattaunawa da bangarorin biyu don sanin makomar dan wasan

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI