Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Tottenham za ta sayi Dybala kan yuro miliyan 70

Paulo Dybala
Paulo Dybala Reuters/Giorgio Perottino
Zubin rubutu: Michael Kuduson
1 Minti

Kungiyar kwallon kafar Juventus dake kasar Italiya ta amince za ta sayar da dan wasan ta, Paulo Dybala ga Tottenham wacce ta taya shi Yuro miliyan 70.

Talla

Dan wasan gaban na Argentina na iya komawa murza tamaula a arewacin Landan gabanin gasar Firimiyar Ingila da za a fara a karshen wannan mako.

Yanzu dan wasan ya shirya tsaf don tattaunawa da Tottenham kan ka’idoji da yarjeniyoyin da suka shafe shi da game da yadda kwantairagin zai kasance.

Dan wasan mai shekaru 25 ya kasance dan wasa mai mahimmanci ga Juventus tun da ya koma kungiyarc daga Perlemo a shekarar 2015, inda ya taimaka mata lashe kofunan gasar Serie A hudu a shekaru hudu da yayi yana taka mata leda.

Amma makomar Dybala ta shiga wani yanayi mai dauke da ayar tambaya tun da ya koma buga wasa inda bai saba bugawa ba sakamakon zuwan Cristiano Ronaldo daga Real Madrid.

Kwallaye 10 ne dan wasan ya ci a dukkan gasanni a kakar wasan da ta gabata, sabanin 26 da ya ci a wacce ta gabace ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.