Wasanni-Kwallon kafa

Zidane ya sake banca Gareth Bale a wasan Madrid da Red Bull

Dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale
Dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale REUTERS/Wolfgang Rattay

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ya sake banca, Gareth Bale inda ya ki sanya shi cikin tawagar Madrid da za ta kara da Red Bull Salzburg a wasan sada zumunta gabanin tunkarar gasar La Liga a mako mai zuwa.

Talla

Cikin wasannin tunkarar sabuwar kaka 5 da Zidane ya jagoranci Real Madrid, wasanni 2 kacal ya sanya Bale yayinda ya yi amfani da shi a matsayin musaya a wasannin da Madrid ta kara da Arsenal da kuma wanda ta kara da Atletico Madrid.

Baya ga Bale da Zidane bai sanya cikin tawagar ta Madrid da za ta kara da Red Bull ba akwai kuma James Rodriguez da Mariano Diaz, ‘yan wasan 2 da Madrid ke son sayar da su a cikin wannan kaka.

Manajan na Real Madrid Zinadine Zidane dai ya sha bayyana cewa baya bukatar Bale a cikin tawagarsa, inda ya ce sayar da dan wasan zai fi yiwa Club din dadi dai dai lokacin da Manajan ke kwadayin sayo Paul Pogba na Manchester United da Christian Eriksen na Tottenham da kuma Donny van de Beek na Ajax.

A cewar Zidane, matukar Madrid na son sayo wadannan ‘yan wasa to dole ne ta sayar da Bale, ko da dai shugaban Club din Florentino Ferez ya dakatar da batun tafiyar Bale din tafiya Jiangsu ta China.

A shekarar 2022 ne dai kwantiragin Bale zai kare da Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.