Wasanni

Lukaku zai koma Inter Milan akan farashin Pam miliyan 74

Romelu Lukaku
Romelu Lukaku AFP/Franck Fife

Inter Milan ta cimma yarjejeniya da Manchester United domin sayen Romelu Lukaku akan farashin Pam miliyan 74.

Talla

A cikin watan Yulin da ya gabata, Manchester United ta yi watsi da tayin Inter Milan na Pam miliyan 54 a matsayin farashin Lukaku.

A jiya Laraba ne, dillalin dan wasan, Federico Pastorello ya yi balaguro zuwa birnin London, a yunkurinsa na warware matsalar da ke tattare da makomar Lukaku.

A bangare guda, Manchester United ta ci tarar Lukaku saboda kin halartar atisaye tare da sauran ‘yan wasan kungiyar, inda a maimakon haka ya je ya yi atisaye tare da tsohuwar kungiyarsa ta Anderlecht a tsawon kwanaki biyu da suka shude.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.