Wasanni

Zidane yayi amai ya lashe kan Bale

Dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale.
Dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale. REUTERS/Andrea Comas

Mai horas da Real Madrid Zinedine Zidane ya yi amai ya lashe dangane da matsayar sa kan makomar dan wasan kungiyar na gaba Gareth Bale.

Talla

A makwannin da suka gabata Zidane ya bayyana karara cewar baya bukatar kasancewar Bale cikin ‘yan wasansa dan haka, za a gaggauta saida shi gawata kungiya; kalaman da a waccan lokacin wakilin Bale ya bayyana a matsayin cin zarafi gare su.

Sai dai a ranar lahadin da ta gabata, bayan wasan sada zumunci tsakanin Real Madrid da AS Roma da aka tashi 2-2 daga bisani Roma ta yi nasara a bugun daga kai sai mai tsaron raga, Zidane ya bayyana Bale da takwaransa dake zaman aro a Bayern Munich James Rodriguez, a matsayin bangare daga cikin kusoshin tawagar ‘yan wasan kungiyar.

Sai dai Zidane ya jaddada cewa komai zai iya faruwa dangane da batun yiwuwar sauyin ‘yan wasan biyu zuwa wasu kungiyoyin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.