FIFA ta ci tarar Manchester City kan sayen 'yan wasa
Wallafawa ranar:
Kungiyar Kwallon Kafa ta Manhester City ta tsallake hukuncin haramta mata sayen ‘yan wasa, amma an ci ta tara bayan ta amince da laifin karya dokokin FIFA na sayen matasan ‘yan wasa.
Yanzu haka, Manchester City wadda ke rike da gambin firimiyar Ingila za ta biya tarar Swiss Francs dubu 370 kwatankwacin Pam dubu 315.
Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta ce, Manchester City ta karya ayar dokarta ta 19 da ke cewa, 'yan wasan da suka zarce shekaru 18 kadai ne, za a iya cefanen su zuwa wata kasa.
A shekarar 2016 ne, Manchester City din ta karya wanna ka’idar.
Idan za a iya tunawa, FIFA ta haramta wa Chelsea cefanen ‘yan wasa har tsawon kakanni biyu saboda karya irin wannan ka’ida.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu