Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

PSG na mana kora- da - hali kan Neymar -Barcelona

Dan wasan PSG Neymar Jr.
Dan wasan PSG Neymar Jr. REUTERS/Lucas Landau
Zubin rubutu: Michael Kuduson
1 Minti

Tattaunawa tsakanin Barcelona da Paris Saint Germaine game da yiwuwar komawar Neymar Spain ta gamu da cikas.

Talla

Kungiyar PSG dai na da niyyar barin Neymar ya bar ta a wannan kaka zuwa Barcelona ko Real Madrid, amma yanzu a tattaunawar da take da Barcelona, tana neman a ba ta ‘yan wasa 3 daga Barcelona, tare da wasu damin damasheren kudade.

Rahotanni dai sun ce wannan bukata da PSG ta mika wa Barcelona ta ruguje tattaunawar, lamarin da ya sa yanzu Real Madrid ke kan gaba cikin masu neman sayen shahararren dan wasan mai shekaru 27.

Barcelona ta harzuka da wannan al’amari, inda take cewa da gangan PSG ke neman lalata wannan ciniki na Neymar, kuma hakan kora – da - hali ne.

Sai dai har yanzu Barcelona ba ta yanke kauna game da samun Neymar ba, saboda ta ce za ta ci gaba da kokartawa har sai ta ga abin da ya ture wa buzu nadi.

Neymar ya ci wa Barcelona kwallaye 105 a wasanni 186 a tsakanin shekarar 2013 da 2017, inda ya taimaka ta lashe kofunan La liga biyu da na zakarun Turai daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.