Wasanni

Van Dijk na gogayya da Messi da Ronaldo

Virgil van Dijk na Liverpool
Virgil van Dijk na Liverpool Reuters

Zaratan ‘yan wasan kwallon kafa da suka hada da Lionel Messi na Barcelona da Cristiano Ronaldo na Juventus da Virgil van Dijk na Liverpool na fafatawa da juna wajen lashe kyautar da hukumar UEFA ke bai wa gwarzon dan wasanta na shekara.

Talla

Za a bayar da kyautar ce ga daya daga cikin ‘yan wasan uku a yayin bikin fitar da jadawalin gasar zakarun Turai ta bana a birnin Monaco a ranar 29 ga watan Agusta.

Van Dijk ya samu damar gogayya da Messi da Ronaldo ne sakamakon bajintar da ya nuna wajen tsare bayan Liverpool har ta lashe kofin zakarun Turai karo na shida a kakar bara.

Messi ne ya fara lashe irin wannan kyauta wadda UEFA ta fara bayarwa a shekarar 2011, sannan Ronaldo ya lashe ta a shekarar 2014 da 2016 da kuma 2017.

A halin yanzu dai Luca Modric ne ke rike da gambin kyautar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI