Wasanni-Kwallon kafa

FIFA ta dakatar da Siasia har abada

Tsohon mai horar da tawagar 'yan wasan Super Eagles ta Najeriya Samson Siasia
Tsohon mai horar da tawagar 'yan wasan Super Eagles ta Najeriya Samson Siasia

Hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA a Juma’ar nan ta dakatar da jami’in hukumar kwallon kafa ta Najeriya, kuma tsohon dan wasan kasar Samson Siasia har na tsawon rayuwarsa bayan kwamitin binciken hukumar ya same shi da laifin karbar rashawa don jirkita sakamakon wasanni.

Talla

A wata sanarwa, kwamitin hukumar ya ce an binciki Samson Siasia ne bayan binciken da ake na wani jami’in wasanni, Wilson Raj Perumel, wanda ya amince da laifin jirkita sakamakon wasanni.

Binciken da aka fara a watan Fabrairu, ya sami Siasia da laifin yarda da cewar zai karbi cin –hanci don a jirkita sakamakon wasanni, abin daya yi hannun riga da dokoki da ka’idojin FIFA, kamar yadda sanarwar ta yi bayani.

Baya ga dakatar da Siasia daga shiga harkokin da suka shafi kwallon kafa har abada abadin, ko har iya tsawon rayuwarsa, an ci shi tarar sa Yuro dubu 46 ko dalar Amurka dubu 50, wato kwatankwacin naira miliyan 18 da ‘yan kai.

Siasia, wanda tsohon dan wasan gaban Najeriya ne, ya horar da babban tawagar kasar na dan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.