Wasanni

Liverpool ta zarta United wajen lashe manyan kofuna

Tawagar kwallon kafar kungiyar Liverpool bayan lashe kofin UEFA Super Cup.
Tawagar kwallon kafar kungiyar Liverpool bayan lashe kofin UEFA Super Cup. AFP/Ozan Kose

Kididdiga ta nuna cewa Liverpool ta zarta abokiyar hamayyarta Manchester United wajen lashe manyan kofuna.

Talla

A halin yanzu Liverpool ta lashe jimillar manyan kofuna 43 yayinda United ke da 42.

Adadin manyan kofunan na Liverpool ya karu ne bayan nasarar lashe UEFA Super Cup, a wasan da suka doke Chelsea da kwallaye 5-4 a bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan kammala fafatawar mintuna 120 a 2-2.

A watan Mayu da ya gabata, adadin manyan kofunan Liverpool yayi dai dai da na Manchester United bayan da Liverpool din ta lashe kofin gasar Zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.