Wasanni-Kwallon kafa

Manchester United ta nuna rashin jin dadi da kalaman batanci kan Pogba

Dan wasan Manchester United Paul Pogba da mai horar da kungiyar Ole Gunnar Solskjaer.
Dan wasan Manchester United Paul Pogba da mai horar da kungiyar Ole Gunnar Solskjaer. REUTERS/Dylan Martinez

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Harry Maguire ya yi kakkausar suka kan kalaman nuna wariyar da ake kan Paul Pogba bayan rashin nasararsa ta gaza zura kwallo a bugun fenaritin da aka bashi yayin wasan United da Wolves wanda suka ji canjaras karkashin gasar Firimiyar Ingila a jiya Litinin.

Talla

A cewar Maguire wanda ya yi kakkausar suka kan caccakar ta Pogba, ya dora laifin zuzuta lamarin kan kamfanonin jarida bisa cewa su ke kirkiro da kalaman tsokana wanda kan juyewa zuwa nuna wariya.

Cikin kalaman Marcus Rashford abokin wasan Pogba, da ya wallafa a shafinsa na Twitter wanda shima ya nuna bacin rai game da nuna wariyar jinsin ga Paul Pogba, ya ce kalaman batanci kan dan wasan Manchester United guda daya tamkar batanci ne ga Club din baki daya.

Shima dai manajan Club din Ole Gunnar Solskjear ya ki sukar Pogba kan barar da bugun fenaritin, inda ya ce Pogba ya zura kwallaye da dama a bugun Fenariti.

Ko a bara ma dai sau 3 Pogba ke barar da bugun fenariti a wasanni daban-daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI