Wasanni

NFF za ta sauya hukuncin FIFA kan Siasia

Samson Siasia
Samson Siasia Reuters

Hukumar Kwallon Kafar Najeriya ta bayyana kaduwarta da matakin da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA ta dauka na haramta wa tsohon kocin tawagar kasar, Samson Siasia shiga harkokin wasanni har abada bisa samun sa da laifin amincewa da karbar rashawa, yayinda NFF ta lashi takobin ganin an sauya wannan hukuncin.

Talla

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, FIFA ta dauki wannan matakin kan Siasia mai shekaru 52 bayan gudanar da bincike mai zurfi kan sauya sakamakon wasa da aka zarge shi da hannu a ciki.

An zargi Siasia da hada baki da Wilson Raj Perumal wanda FIFA ta same shi da hannu dumu-dumu wajen sauya sakamakon wasanni, abinda ya sa jami’an tsaro suka kama shi.

Siasai ya musanta aikata ba daidai ba, yana mai cewa, zai wanke kan sa.

A halin yanzu, hukumar NFF ta Najeriya ta ce, ta mika rahoton FIFA ga lauyoyinta domin nazari kafin daukar matakin ganin an janye wannan hukuncin mai tsauri kan Siasia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI