Wasanni-Kwallon kafa

Coutinho na son komawa Bayern Munich dungurugum

Philippe Coutinho bayan kammala kulla kwantiragin shekara guda a matsayin aro da Bayern Munich
Philippe Coutinho bayan kammala kulla kwantiragin shekara guda a matsayin aro da Bayern Munich Michael Dalder/Reuters

Tsohon dan wasan Barcelona da ya amince da kulla kwantiragin shekara guda a matsayin aro tare da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich Philippe Coutinho ya nuna sha’awar daukar lokaci mai tsawo ya na taka leda da a Jamus.

Talla

Cikin kalaman Coutinho bayan isarsa Munich, abubuwa da dama basu tafi yadda ya yi tsammani a Barcelona ba, a don haka ya na fatan taka leda a bangaren Bayern Munich dungurugum.

Dama dai karkashin yarjejeniyar aron Coutinho kan yuro miliyn 8 da rabi Bayern Munich na da zarafin iya sayenshi baki daya kan yuro miliyan 120 bayan ya kammala wa’adinsa na shekara guda a matsayin aro.

Coutinho dan Brazil mai shekaru 27 ya ce yana fatan bayar datasa gudunmawar wajen ganin Bayern Munich ta dage kofuna da dama yayin zamansa a Club din.

Tun bayan sayo Coutinho daga Liverpool kan yuro miliyan 142 Cikin watan Janairun 2018 Barcelona ta ce bata gamsu da salon takun Coutinho ba duk kuwa da yadda ya zura mata kwallaye 21 a wasanni 76.

Ana dai ganin bayar da aron Coutinho na daga cikin shirye-shiryen Barcelonar na dawo da tsohon dan wasanta Nerymar Junior daga PSG ta Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI