Wasanni

Messi ne ya haddasawa Coutinho matsala a Barcelona - Rivaldo

Lionel Messi da Philippe Coutinho yayin murnar nasarar jefa kwallo a raga.
Lionel Messi da Philippe Coutinho yayin murnar nasarar jefa kwallo a raga. Reuters

Tsohon dan wasan Barcelona Rivaldo ya zargin kaftin din kungiyar na yanzu, Lionel Messi, da taka rawa wajen haddasa rashin nasarar Philippe Coutinho a kungiyar.

Talla

A watan Janairu na shekarar 2018, Coutinho ya koma Barcelona daga Liverpool kan euromiliyan 148, sai dai har yanzu, jagororin kungiyar Barcelona basu gamsu da kwazon dan wasan ba.

Rashin taka rawar ganin Coutinho ya sa a halin yanzu ya koma kungiyar Bayern Munich tsawon shekara 1 a matsayin aro, kan euro miliyan 8.5, da kuma zabin komawa kungiyar din din din kan euro miliyan 120.

Yayin tsokaci kan halin da Coutinho ya tsinci kansa, Rivaldo, tsohon tauraron Barcelona, yace mamaye al’amuran da Messi yayi ba tareda baiwa Coutinho dama shi ne ya haddasa gazawar da dan wasan yayi wajen cika burin ganin ya maye gurbin tsohon kaftin din kungiyar ta Barcelona, Andres Iniesta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI