Griezman ya zurawa Barcelona kwallo 2 a wasansu da Real Betis

Antoine Griezman yayin wasan da Barcelona ta lallasa Real Betis da kwallaye 5-2
Antoine Griezman yayin wasan da Barcelona ta lallasa Real Betis da kwallaye 5-2 si.com

Sabon dan wasan Barcelona Antoine Griezman ya yi nasarar zura kwallaye har biyu a wasan da suka lallasa Real Betis da kwallaye 5 da 2 a jiya Lahadi karkashin gasar Laliga, kwallayen dake matsayin na farko da ya zura a wasannin Lig tun bayan sayenshi.

Talla

Tun cikin watan Yulin da ya gabata ne Barcelonar ta sayo Griezman daga Atletico Madrid kan yuro miliyan 107 amma kuma ya gaza tabuka abin kirki a wasansu da Athletic Bilbao dai dai lokacin da ‘yan wasan gaba na Club din da suka kunshi Lionel Messi da Luis Suarez da kuma Ousmane Dembele ke jinya.

Yayin wasan na jiya dai bayan kwallayen 2 na Griezman a minti na 41 da kuma 50 da fara wasa, Carles Perez nay z zurawa Barcelona kwallonta na 3 a minti na 56 kafin Jordi Alba da Arturo Vidal su zura kwllaye na 4 da na biyar.

A farkon wasan dai Real Betis ce ta fara zura kwallo cikin minti 15 da fara wasa ta hannun dan wasanta Nabil Fekir, haka zalika ita ta rufe wasan da kwallonta na biyu a minti na 90 ta hannun dan wasanta William Carvalho.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.