Wasanni-Kwallon kafa

Mbappe da Cavani sun samu rauni a wasan da PSG ta lallasa Tolouse

'Yan wasan PSG Edinson Cavani, Kylian Mbappe da kuma Neymar.
'Yan wasan PSG Edinson Cavani, Kylian Mbappe da kuma Neymar. FRANCK FIFE / AFP

‘Yan wasan gaba na PSG 2 Kylian Mbappe da Edinson Cavani sun samu raunuka a wasansu na jiya da suka lallasa Tolouse da kwallaye 4 da banza karkashin gasar Lig 1 ta Faransa.

Talla

Tun a minti na 14 da fara wasa ne aka cire Cavani daga fili tare da maye gurbinsa da Eric Maxim wanda yayi nasarar zura kwallon farko a minti na 50 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

A bangare guda shima Mbappe ya fice daga filin bayan dawowa daga hutun rabin lokaci sakamakon samun rauni a cinya.

Bayan kwallon Maxim daga PSG dan wasan Toulouse Mathieu Goncalves da kansa ya zurawa kungiyarsa kwallo cikin rashin sani a minti na 55 kafin daga bisani Eric Maxim ya kara kwallo ta biyu a minti 75 kana Marquinhos ya karkare da kwallo ta 4 a minti na 83.

Yayin wasan na jiya dai wanda ya gufana ba tare da Neymar Junior na Brazil ba, anga yadda Angel di Maria na PSGn ya barar da bugun fenaritin da aka bashi.

Nasarar ta PSG a jiyan dai ta bai wa Club din damar zamowa na 3 a teburin Lig 1 kasa da Lyon da Rennes wadda ta lallasa PSGn makon jiya da kwallo 2 da 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI