Wasanni-Kwallon kafa

Isco na Madrid zai yi jinyar rauni gabanin wasansu da Villareal

Dan wasan tsakiya na Real Madrid Isco
Dan wasan tsakiya na Real Madrid Isco REUTERS/Juan Medina

Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Isco zai rasa manyan wasannin Laliga da ke gaban Club din cikin wata mai kamawa bayan samun rauni a cinya.

Talla

Club din na Real Madrid mai doka gasar Laliga da kansa ne ya fitar da sanarwar raunin na Isco a yau Laraba amma ba tare da bayyana kwanakin da dan wasan zai dauka ya na jinya ba.

Isco wanda ke matsayin ‘yan gaba-gaba a jerin ‘yan wasan da mai horar da kungiyar ta Real Madrid Zinadine-Zidane ke amfani da su a kusan kowanne wasa, akwai bayanan da ke nuna cewa zai rasa wasannin Real Madrid da Villarreal haka zalika na Real Madrid da Levante ranar 14 ga watan Satumba mai zuwa.

Raunin na Isco dai kari ne kan ‘yan wasa kusan 5 da yanzu haka ke jinya a Real Madrid, wadanda suka kunshi Eden Hazard da James Rodriguez da Brahim Díaz da kuma Rodrygo baya ga Marco Asensio.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.