Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Manchester United na shirin bayar da aron Sanchez ga Inter Milan

Dan wasan Manchester United Alexis Sanchez
Dan wasan Manchester United Alexis Sanchez REUTERS/Scott Heppell
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 min

Kungiyoyin kwallon kafa na Manchester United da Inter Milan na ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar aron Alexis Sanchez har yanzu sun gaza cimma jituwa game da albashin dan wasan.

Talla

Sanchez dan kasar Chile mai shekaru 30 wanda ke karbar albashin yuro dubu dari 4 kowanne mako a Manchester United, a makon jiya InterMilan ta mika tayin biyansa yuro dubu 150 amma United ta ki amincewa.

Karkashin yarjejeniyar karbar aron Sanchez din dai Inter Milan taki amincewa da bukatar sayensa bayan karewar wa’adin aron na san a shekara guda.

Matukar dai yarjejeniya ta kullu tsakanin kungiyoyin biyu hakan na nufin Sanchez zai bi sahun Romelu Lukaku da ya koma Inter Milan daga Manchester United cikin wannan kaka kan yuro miliyan 74.

Cikin watanni 19 bayan komawar Sanchez Man United daga Arsenal kwallaye 5 kacal ya zura a wasanni 45 da ya taka leda a ciki.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.