Wasanni

Har yanzu Zidane na sa ran kulla yarjejeniya da Pogba

Zinedine Zidane yayin gaisawa da Paul Pogba a Amurka cikin shekarar 2016.
Zinedine Zidane yayin gaisawa da Paul Pogba a Amurka cikin shekarar 2016. Chema Rey/MARCA

Rahotanni daga Spain sun ce har yanzu kocin Real Madrid Zinaden Zidane, yana sa ran kulla yarjejeniya da tauraron Manchester United Paul Pogba, kafin rufe hada-hadar sauyin shekar ‘yan wasa a nahiyar Turai, ranar 2 ga watan Satumba.

Talla

An dai shafe tsawon lokaci ana alakanta Pogba da shirin komawa Real Madrid a kakar wasa ta bara, musamman bayan da dan wasan da kansa ya bayyana aniyar sauya shekar zuwa Spain, sai dai har yanzu kungiyar ta Real Madrid ba ta gabatar da tayin sayen Pogba ba a hukumance.

Manchester Uniteddai ta tsayar da farashin fam miliyan 180 ga duk kungiyar dake muradin kulla yarjejeniya da Pogba, farashin da ake ganin ya yiwa Real Madrid tsauri, la’akari da cewa zuwa yanzu ta kashe sama da fam miliyan 300, wajen sayen ‘yan wasan da suka hada da Eden Hazard, Luka Jovic da kuma Eder Militao.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.