UEFA ta fitar da sabon jadawalin gasar cin kofin zakarun Turai
Wallafawa ranar:
Hukumar kwallon kafar Turai ta fitar da sabon jadawalin gasar cin kofin zakarun Turai, a wasannin gasar da za su fara daga 17 ga watan satumba mai kamawa zuwa ranar 30 watan Mayun 2020.
A rukunin farko na jadawalin wato rukunin A wanda ya kunshi kungiyoyin kwallon kafa 4 akwai PSG ta Faransa da Real Madrid da Club Bruges da kuma Galatasaray.
A rukunin B kuwa akwai Bayern Munich da Tottenham, da Olympiakos baya ga Red Star Belgrade.
Sai rukunin C da ya kunshi Manchester City da Shakhtar Donetsk da kuma Dinamo Zagreb baya ga Atalanta.
Akwai kuma rukunin D da ya kunshi Juventus da Atletico Madrid sai Bayer Leverkusen da kuma Lokomotiv Moscow.
Sai rukunin E da ya kunshi Liverpool mai rike da kambun na zakarun Turai sannan Napoli kana Salzburg, da Genk.
Akwai kuma rukunin F da hadar da Barcelona, Borussia Dortmund, da Inter Milan da kuma Slavia Prague.
Sai rukunin G da yakunshi Zenit St Petersburg da Benfica da Lyon da kuma RB Leipzig.
Kana rukunin H kuma na karshe da ya kunshi Chelsea, Ajax da Valencia kana Lille.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu