Faransa-Wasanni

Rauni zai hana Pogba taka leda a wasan Faransa da Albania

Paul Pogba yayin wasansa a bangaren Faransa
Paul Pogba yayin wasansa a bangaren Faransa REUTERS/Michael Dalder

Tawagar kungiyar kwallon kafar Faransa, ta fitar da sunan Paul Pogba daga jerin ‘yan wasan da za su taka leda a wasannin neman gurbin shiga gasar EURO 2020 da kasar za ta kara da Albania da Andorra a ranakun Asabar da Talata mai zuwa.

Talla

Matakin dai ya biyo bayan raunin da Pogba ya samu ko da dai dan wasan ya buga ilahirin mintuna 90 na wasan da Manchester United ta yi canjaras da Southampton a ranar Asabar ko da dai ya fita daga fili yana dingishi, kazalika mai horar da kungiyar ya ce suna fata dan wasan ya taka leda a wasansu da Leicester City ranar 14 ga watan nan.

Tuni dai kungiyar kwallon kafar ta Faransa, ta aike da sakon Twitter inda ta ke yiwa Pogba fatan samun sauki inda ta sanar da sunan dan wasan gaba na Arsenal Matteo Guendouzi a matsayin wnada zai maye gurbinsa.

Wannan dai ne karon farko da Matteo Guendouzi mai shekaru 20 zai takawa tawagar manya ta kungiyar kwallon kafar Faransa leda.

A cewar Mai horar da kungiyar kwallon kafar Faransar Didier Deschamps zai fi kyautuwa ga Pogba ya yi jinyar kafarsa maimakon tilasta kansa ga shiga wasannin biyu.

Baya ga Pogba dai ‘yan wasa irinsu Aymeric Laporte, Ousmane Dembele da Kylian Mbappe baza su taka leda a wasannin biyu ba saboda rauni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI