Isa ga babban shafi
Wasanni

"Alakanta Lukaku da biri jinjina ce a gare shi"

Romelu Lukaku na Inter Milan
Romelu Lukaku na Inter Milan Reuters
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 min

Kungiyar Magoya Bayan Inter Milan ta ce, kukan birin da magoya bayan Kungiyar Kwallon Kafa ta Cagliari suka yi wa Romelu Lukaku, wani nau’i ne na girmama shi amma ba cin zarafin sa ba.

Talla

Sanarwar da kungiyar magoya bayan ta fitar, ta ce, masoya kwallon kafa a Italiya ba sa nuna wariyar launin fata, sannan cin zarafin da aka yi wa Lukaku na cikin wasa.

A cewar sanarwar, magoya bayan Cagliari na fargabar kwarewar Lukaku ta jefa kwallaye a ragarsu, abinda ya sa suka fara yin kukan biri domin daburta masa lissafi a yayinda yake shirin buga fanaritin da aka bai wa Inter Milan.

Kodayake kungiyar ta bai wa Lukaku hakuri kan cin zarafin, tana mai jaddada masa cewa, Italiya ba kamar sauran kasashen Turai ba ne da ke fama da matsalar wariyar launin fata.

Lukaku wanda ya koma Inter Milan daga Manchester United, ya jefa kwallon da ta bai wa kungiyarsa nasara da ci 2-1 a yayin wasan nasu da Cagliari.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.