Isa ga babban shafi
Wasanni

Afirka da Asiya sun gaza a gasar kwallon kwando ta duniya

kwallon kwando
kwallon kwando Open access/Reisio
Zubin rubutu: Michael Kuduson
2 min

Ba za a dama da kasashen Afirka da Asia a zagaye na biyu na gasar kwallon kwandon duniya ta bana da ke gudana a kasar China ba.

Talla

Wannan ce gasar kwallon kwando na duniya mafi girma tun da aka fara gasar amma babu wata tawaga daga Afirka ko Asia da ta samu tsallakewa zuwa zagaye na biyu a cikinta.

Duk da cewa ita ce mai masaukin baki, kuma duk da yawan al’ummarta da ya kai biliyan 1 da miliyan dari 4, China ta rikito a jiya Laraba, bayan kashi da ta sha a hannu Venezuela da ci 72 – 59.

Wannan na zuwa ne sa’o’i bayan Tunisia ta kasa kaiwa ga gaci sakamakon doke ta da Puerto Rico ta yi da kyar da ci 67 -64.

Najeriya ta yi wa Koriya ta Kudu dukan-kawo wuka da ci 108 – 66 a daidai lokacin da wadancan kasashen ke shan duka gun abokan karawarsu, amma duk da haka ta rikito saboda ba ta yi nasara a wasanni biyu da ta yi na bude gasar ba.

Rabon da a fafata a zagaye na biyu na wannan gasa ba tare da wakilci daga Afirka ko Asia ba tun a shekarar 1998, lokacin da tawagogi 16 ne kawai ke barje gumi a gasar.

Yanzu tawagogi 32 ne ke fafatawa a gasar, amma sai dai kasashe daga yankin Amurka da Turai ne kawai suka saura a gasar, karkashin jagorancin mai rike da kambun, Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.