Isa ga babban shafi
Wasanni

Kwamitin Olympic na 2020 a Japan zai yi gwajin dusar kankara da ya samar.

Tambarin gasar Olympic ta duniya
Tambarin gasar Olympic ta duniya Reuters/Mike Blake
Zubin rubutu: Michael Kuduson
2 min

Kwamitin shirya gasar Olamfik da za a yi a birnin Tokyo na kasar Japan, wato Tokyo 2020, ya samar da komai don ganin ba a ji jiki daga yanayi mai tsanannin zafi na birnin a lokacin gasar ba, kuma yanzu yana so ya samar da dusar kankara, wato snow.

Talla

Kwamitin shirya gasar Olamfik da za a yi a birnin Tokyo na kasar Japan, wato Tokyo 2020, ya samar da komai don ganin ba a ji jiki daga yanayi mai tsanannin zafi na birnin a lokacin gasar ba, kuma yanzu yana so ya samar da dusar kankara, wato snow.

A Alhamis din nan kwamitin ya tabbatar da cewa yana shirin yin gwajin dusar kankara, wato snow da ya samar a wani biki nan gaba a wannan watan da muke ciki, a kokarin da yake na samar da yanayi mai sanyi da armashi ga ‘yan kallo da ‘yan wasa yayin gasar, sakamakon zafi da birnin Tokyo ya saba yi a daidai watan da za a yi gasar.

Wata kakakin kwamitin shirya gasar ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, za a watsa dusar kankarar da aka samar a kujerun ‘yan kallo da ma daidai inda rana ke haskawa a yayin gwajin ranar 13 ga watan Satumba.

Kwamitin yana ta aiki tukuru ganin cewa a lokacin yanayin zafi ne za a gudanar da wannan gasa, wato lokacin da yanayi ke kaiwa har digiri 35 na centigrade a birnin Tokyo, kuma hakan zai kasance da hadarin gaske ga ‘yan wasa da ’yan kallo.

An riga an yi gwajin matakai da dama da suka hada da kirkiro tashar samar da danshi, da tantuna masu na’urar sanyaya daki, wato AC, da kuma tukwane na fure, wanda ake ganin zai taimaka wajen dadada wa ‘yan kallo.

Japan ba ta dauki nauyin gasar Olamfik ba tun bayan shekarar 1964, wadda a lokacin ma watan a Oktoba aka yi gasar don kauce wa yanayi na zafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.